An kama wani mutum da ake zargin ya kashe sugar mummynsa da kuma sace mata mota a Enugu


Yan sanda da ke aiki a sashin kisan kai na CID na jihar Enugu, a ranar 8 ga Nuwamba, sun kama wani Osuagwu Chidubem (namiji) a Nekede Owerri, a lokacin da yake yunkurin siyar da wata mota kirar Toyota Corolla da ake zargin ya sata daga wajen masoyiyar sa Amarachi Chukwu mai shekaru 32, bayan zargin kashe ta a gidanta dake Meniru, Awkunanaw, Enugu a ranar 1 ga Nuwamba.


Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya ce binciken da ‘yan sandan suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin da ‘yan tawagarsa ne da safiyar ranar da aka ambata sun hada baki suka tafi gidan matar. wacce aka kashe, ta yi yunkurin kwace mata mukullin motar ta kirar Toyota Corolla, wanda ta ki yarda.


 ''Bayan tsayin daka sai suka daure hannayenta da kafafuwanta da bakinta da tufafi; ya kulle ta cikin gidan sannan ya fice da motar. Sai dai an gano gawarta a gidan da aka ce a ranar 4 ga Nuwamba, bayan da Jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin ‘yan sanda na Ikirike na rundunar suka bude kofar, bayan samun rahoton cewa wani wari na fita daga cikin gidan.


 Jami’an hukumar sun kwashe gawar zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta, sannan aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa domin adanawa da kuma tantance gawar,” Ndukwe ya ce.


Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa sakamakon haka an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincikensa kuma an tsare shi a gidan kurkuku har zuwa ranar da za'a ci gaba da sauraron karar.


Ko a makon da ya gabata irin hakan ta faru a Jihar katsina inda aka kama wani matashi kan zargin sa na kashe abokinsa domin kawai ya mallaki motarsa. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post