Yanzu-Yanzu Kotu Ta Aike Da Matashin Da Yaci Zarafin Aisha Buhari Gidan-Yari


A ranar Talata ne aka hangi Aminu Muhammad a gaban kotu bisa zarginsa da cin mutuncin matar shugaban kasa Aisha Buhari inda Kotun ta aike shi gidan yari. 


Shafin BBC ya rawaito cewa lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar da cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja babban birnin kasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.


Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.


''Ko a zaman kotun da ya gabata a ranar Talata mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.''


''Akan haka muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,'' in ji CK Agu.


Tun da farko iyayen dalibi Aminu Muhammad sun fada wa BBC cewa za a gurfanar da dan nasu kotu yau Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman jiya Talata, kuma za a sake wani zaman yau ko gobe don duba bukatar ba da shi beli.


Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace '' yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.''


Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba.


Shi dai Aminu Muhammad an kama shine akan zargi da cin mutuncin matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post