Yanzu-Yanzu: Kakar Darakta Falalu A Dorayi Ta Kwanta Dama


INNA lillahi wa inna ilaihir raji'un! Allah ya yi wa kakar jarumi kuma darakta a masana'antar Kannywood, Falalu A. Ɗorayi, rasuwa. Hajiya Amina, wadda ake kira Nene ko Yakumbo ko Yadikko, ta rasu a yau a Kano. 


Marigayiyar ta rasu ta na da shekara 110 a duniya. A sanarwar rasuwar da Falalu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa za a yi jana'izar ta ranar Talata da ƙarfe 12 na rana a Gidan Maƙera da ke unguwar Ja’en Ɗorayi.


Da fatan Allah ya yi mata rahama, Allah ya kyautata makwancin ta, amin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post