Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya samu karuwar diya mace da matarsa ​​ta hudu


Tsohon sarkin Kano Maimartaba Sunusi Lamido Sunusi shi da matarsa ta hudu Hajiya Sa’adatu Barkindo sun yi murnar samun karuwar 'ya mace. 


Bayan haifar yarinyar an saka wa mata suna Zainab (Khausar). 


Tsohon sarkin ya auri Sa’adatu, diyar Barkindo Aliyu Mustapha, Lamidon Adamawa a shekarar 2015 lokacin yana sarkin Kano. 


Sun haifi ɗansu na farko tare a ranar 5 ga Mayu, 2020.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post