Yadda wani mahaifi ya baiwa 'yarsa kayan maye ta sha daga bisani kuma yaimata fyade


Jami'an tsaro sun yi nasarar kame wani mahaifi da ake zargin sa da baiwa ƴarsa ƙwaya don ta fita daga hayyacin ta daga bisani kuma yai mata fyaɗe.


So-Safe itace ƙungiyar tsaron da suka kame magidancin mai shekaru 50 da haihuwa dan asalin jihar Ogun a yankin karamar hukumar Ifo ta Jihar a ranar Alhamis.


Moruf Yusuf wanda shine kakakin rundunar tsaron ya shaidawa manema labarai a ranar juma'a cewa rundunar su ta samu wani kiran gaggawa cewa wani mutum ya yiwa ƴar cikinsa fyaɗe.


Sai dai bayan da rundunar mu ta isa wajen da lamarin ya faru sai da aka sha wuya kafin a kwaci mutumin daga hannun matasan unguwar bayan sun samu labarin abinda ya aikata.


Yarinyar da aka boƴe sunanta ta bayyana cewa wannan ba shine karon farko da mahaifin nata yake aikata mata hakan ba wannan karon ne dai asirinsa ya tonu.


Kawo yanzu dai rundunar tsaron ta miƙa wanda ake zargin ga hannun ƴan sanda domin ƙara bincike akansa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post