Uba Ya Gargadi Dansa Da Kada Ya Auri 'Yar Talaka Don Basu San Komai Ba Sai Son Abin Duniya


Idan ana batun soyayyar gaskiya to babu maganar kudi a ciki, sai dai a wannan labarin lamarin ba haka yake ba domin wani uba ne ya gargadi dansa da kada ya kuskura ya auri' 'yar talaka kamar yadda Jaridar labaran Hausa ta rawaito. 


Mahaifin a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yace dalilin da yasa ya fadawa dansa cewa kada ya auri 'yar talakawa domin shi hakan ya faru dashi kuma daga baya ya gano kuskurensa, don haka baya so hakan ya Kara faruwa da dansa. 

 

Ya kara da cewa 'ya'yan talakawa suna da matsala sosai domin idan suna soyayya da mai kudi basa duban komai sai kudin da kake dashi so suke kawai su aure ka su ci kudin ka domin basa yi soyayya tsakani da Allah. 


Hakan yasa na shawarci dana da kada ya kuskura yai soyayya da 'yar talaka domin ba su iya ba kuma basu santaba. Burinsu kawai su kubuta daga halin da suke ciki na tsantsar talauci da suke ciki, cewar mahaifin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post