Tarihin Rayuwar Hauwa Garba, Sabira Gidan BadamasiHauwa Garba wacce aka fi sani da ƴar Auta a yanzu kuma ake kira da Sabira a cikin shirin Gidan Badamasi mai dogon Zango da tashar Arewa 24 suke haskawa.


Hauwa Garba dai ƴar asalin garin Bichi ce wani local government dake cikin jihar Kano. Anan aka haifeta anan ta yi karatu matakin Firamare har zuwa Sakandire.

 

Kuma a garin su ta yi aurenta na fari. Kawo yanzu dai Sabira ta yi aure har sai uku kuma ta haihu sau biyu sai dai guda daya ya rasu yanzu sai guda ɗaya ne a raye.

Sabira kwana casa'in

Daya daga cikin mijin da ta aura a baya har da tsohon jarumi marigayi Alh. Rabilu Musa Ibro wanda suka yi aure a shekarar 2004 sun shafe shekaru biyu tare. Kuma sun samu karuwar haihuwa ta yaro mai suna Mohd Arfat,sai dai wata shida yai a duniya ya rasu.


Kafin shigarta harkar film Sabira ta yi dirama irin na daɓe wanda daga baya ta hadu da su Ɗan Auta, Baba Ari, Cinnaka da suka je katsina har suka haɗu da Sabira suka yi mata tayin shiga sana'ar film.


Sabira ta fara fitowa a sabon film mai suna "SAKARKARU". wanda kuma tun bayan wannan film din ta yi finafinai da dama wanda ita kanta ba ta san adadinsu ba.

Sabira kwana casa'in

Sabira ta bayyana cewa ba ta samu wani kalubale daga wajen iyaye ko dangi ba tun bayan Da ta fara fitowa a finafinan Hausa. Kawo yanzu ta shafe sama da shekaru 14 cikin sana'ar film.


Salon irin kwalliyar da Sabira take yi a cikin finafinan Hausa ya ja hankalin mutane wanda wasu da dama basu san ainihin yadda kamaninnta na zahiri suke ba.


Sabira ta ce ta samu nasarori sosai a harkar film domin kuwa jama'a suna sonta, sannan akwai manyan mutane wanda ba ta yi tunanin za su santa ba har kiranta suke yi suna yi mata kyauta.

Ta bayyana irin girmamawa da take samu daga wajen abokan sana'arta ta film. Ta ce suna bata girma sosai. Tace suna zaune lafiya da kowa tare da girmama juna domin ba ta taɓa samun matsala da kowa daga cikinsu ba.


Sabira ta bayyana abinda ke sakata fushi ba ta yi abuba sai ace ta yi, abin yana damunta. zuwa yanzu Sabira tana da shekaru 39 a duniya. Ta bayyana ƴarta itama ta fara fitowa a cikin finafinan Hausa.

Sabira kwana casa'inSabira kwana casa'in


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post