KWANKWASO: Zan inganta Ilimi daga matakin Firamare Har zuwa Jami'a


Dan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, yasha alwashin inganta ilimi a fadin kasa Najeriya daga matakin makarantun Firamare har izuwa Jami'a.


Kwankwason ya baiyyana hakanne a yayin da yake bude sabuwar sakatariyar jam'iyyar sa ta NNPP, a ranar lahadi a unguwar Sharada dake jihar kano.


Inda ya kara da cewa "zai tabbatar ya samawa dukkan wasu matasa da suka kammala karatun su na Jami'a aiki idan ya dare kujerar shugabancin taraiyyar Najeriya".


Kwankwaso yaci gaba da cewa" zan cigaba da tsarin da nake na daukar nauyin karatun Hazikan dalibai zuwa kasashen waje domin karo karutu da zai kawo cigaba a Najeriya dama habakar tattalin Arziki. 


Daga Umar Saleh Zara

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post