Jam'iyar APC Ta Naɗa Matar Shugaban Kasa Aisha Buhari Matsayin Shugabar Kamfen Din Tinubu


Tun gabanin fara bayyana yaƙin neman zaɓe a   hukumance jam'iyyu da dama suka fitar da waɗanda za su yi musu yaƙin neman zaɓensu. Mata ana kallon su a matsayin wanda suka fi bayar da gudummawa wajen kada kuri'a.


Jaridar Legit Hausa ta rawaito cewa, Jam'iyar APC ta sanar da Aisha Buhari a matsayin wacce za ta yi musu yaƙin neman zaɓe a ɓangaren mata a zaɓe mai zuwa na 2023. Rinsola Abiola, diyar marigayi Cif MKO Abiola, kuma jigo a jam’iyyar APC itace ta fitar da sanarwar a ranar Asabar.


Akwai kuma sauran mata da aka bayyana sunayensu da za su taimakawa Aisha Buhari kamar Nana Shettima, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Borno kuma uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa jam'iyyar APC da kuma Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltan Legas ta tsakiya a zauren majalisar dattawa a wa'adi na uku a majalisar dattawa kuma tsohuwar uwargidan tsohon gwamnan jihar Legas.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post