Yadda Zaku Samu Kyautar Data 5GB Akan N500 Kacal, Sabon Tsari Mafi Sauki


Data ta zama tamkar wani abinci, duba da yadda a kullum miliyoyin mutane ke amfani da ita wajen gudanar da ayyukan su na yau da kullum a wayoyinsu da kwamfuta. Hakan yasa muke sayan tsarin data don gudanar da wannan ayyukan da muke yi da wayoyin mu. 


Akwai wani tsari da kamfanin MTN suke dashi da zaka kashe N500 ka samu 5GB. Shiyasa muka kawo muku shi domin kuma ku amfana duk da nasan cewa mutane da suka San wannan tsarin kadan ne. 


MTN yana gaba-gaba wajen masu yawan yin amfani dashi domin sadarwa a Najeriya da kuma sassan kasashen Afrika. Domin kuwa suna da tsare-tsare data masu sauki da suke samarwa masu amfani dashi. 


Wannan tsarin dai ya bambanta da sauran tsare-tsaren da aka saba gani da MTN suke yi.  Idan baka amfani da MTN to kayi kokari ka gwada wannan tsarin. 


Abin Lura: Ga duk wanda yakeson ya shiga wannan tsarin ka tabbatar da cewa kana dauke da manhajar application na MTN, Idan bakada shi zaka iya dauko shi daga play store 


Domin samun damar shiga tsarin data 5GB akan Naira 500 akan layin MTN, ga abubuwan da zaku yi ku samu.


Wayar hannu (Android ko iOS) mai dauke da Intanet

 MTN Sim Card mai aiki

 Naira 500 a kan katin SIM na MTN 

Yanzu, ba tare da tsayawa ba, bari mu kalli yadda za ku iya samun 5GB akan tsarin data na MTN 500.

Idan kunaso ku shiga tsarin na 5GB akan Naira 500 akan MTN Ku tabbata kun kunnna Data wayar hannu ku akan Na'urar Android ko iPhone 

Shiga zuwa Google PlayStore ko Apple AppStore, ku rubuta "MTN App." 

Idan ya fito muku dashi sai ku taba ku danna download, Idan ya gama zai sauka akan wayar ku 

Bayan kun ya application din yazo kan wayarku sai ku bude shi. 


Yi amfani da lambar wayar ku ta MTN don shiga cikin dashboard ɗin ku 


A cikin dashboard ɗin ku, za ku ga wani waje da aka rubuta "offers" sai ku danna " za kuga ansa continue." za ku sayi data daga kudin dake akan lambar wayar ku. 


Kuna yin hakan sai ku fita kuje kan layikun ku duba adadin data da kuka samu ta 5GB. Za kuyi amfani da *131*4#


Abin Lura : Shi wannan tsarin kawai ana amfani dashi ne a ranar Talata kawai, sauran kwanaki tsarin baya yin aiki. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

2 Comments

Previous Post Next Post