Yadda Aka Tsinci Gawar Jariri Sabon Haihuwa An Jefar Dashi A Cikin Shara Da Ransa


Hukumar tsaro ta 'yan sanda a jihar Lagos ta tabbatar da tsintar wani jariri sabon haihuwa wanda ake zargin mahaifiyarsa ce ta jefar da shi a wata bola cikin birnin na Lagos. 


SP Benjamin Hundeyin shine mai magana da yawun hukumar 'yan Sanda ta jihar Lagos ya bayyanawa cewa an tsinci jaririn ne a cikin wata leda kuma aka saka shi a kwandon shara. 


Aminiya ta rawaito cewa Hundeyin ya wallafa hoton jaririn a kan shafinsa na Twitter inda ya Kara da cewa an tsinci jaririn ne a ranar Alhamis. Sai dai bai bayyana unguwar da aka samu jaririn ba. 


Sai dai yace sun yi kokarin ceton jaririn inda yace da ba su yi saurin dauko shi ba da zai iya rasa ransa. Amma yanzu haka jaririn yana cikin koshin lafiya, cewar Hundeyin.


Hundeyin ya yi kira ga mata da su daina yin wannan dabi'a ta jefar da jarirai domin hakan ba hali ne mai kyau ba. Ya ce Akwai mamaki mace ta dauki ciki har tsawon watanni tana dawainiya dashi kuma daga ƙarshe ta jefar da shi.


Jefar da jarirai a Najeriya dai ya zama ruwan dare gama duniya. Domin kuwa duk shekara ana samun ƙaruwar yawan adadin jarirai masu yawa da ake jefar da su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post