Takaitaccen Bayani A Kan Kasuwancin Yanar Gizo, Muhimman Abubuwan da ya Kamata ka Sani


An sha yi min tambaya game da wannan abun da ake kira Online Business, amma duk da ina bayar da amsa a takaice ko kuma nuni ga wasu littatafaina don samun karin haske, na yi tunanin tsakuro wannan takaitaccen bayanin don dalilai guda uku:

i. Yin bayani ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata mu sani


ii. Kore wa mutane shakku game da shi bisa ga wani abu da suke tunani shi ne alhali ba haka ba ne


iii. Nuna bambancinsa da harkokin damfare-damfaren yanar gizo 


Gundarin kalmar Online Business tana nufin Kasuwancin Yanar Gizo, amma tana da ma'ana fiye da daya kamar yadda za mu gani a wannan bayanin.


Hanyoyin samun kudi a yanar gizo ta online business guda uku ne:


1. Kasuwancin Saye da Sayarwa;

A wannan matakin kamar dai kasuwancin zahiri haka abun yake, mutane suna sayen kaya kuma su sayar da su a yanar gizo cikin sauki.


Sai dai akwai ire-iren kayayyakin da ake cinikinsu kamar haka:


i. Kayayyakin Zahiri: wadannan irin kayayyakin su ne kamar shadda, kayan sawa, wayoyi, gidaje, motoci, da sauransu. Daman wadanda suka kasance suna kasuwancinsu a zahirance su suke irin wannan kasuwancin.


Suna daukar hotunan hajojinsu su tallata a social media da wurare da dama a yanar gizo don samun kwastomomi. 


ii. Kayayyakin Lantarki: wadannan kuma su ake kira digital stuffs, digital products, digital items ko kuma online items duk abu daya suke nufi. Irin wadannan kayayyakin sun hada da eBooks, apps, websites, crypto coins, social media accounts, templates, YouTube channels, Facebook pages/groups da sauransu. Mutane suna shiga wannan sana'ar ta saye da sayarwan digital items wato kayayyakin lantarki don su samu abun yi.


To wannan shi ne kasuwancin yanar gizo na mataki na farko. Wannan shi ne online business na saye da sayarwan kayayyaki, daidai ne ba shi da matsala.


2. Aikin Kwadago

Hanya ta biyu kuma da mutane suke amfani da ita a karkashin online business su samu kudi ita ce aikin kwadago, wato freelancing a turance. Aikin kwadago ko freelancing shi ne aikin da za ka yi wa wani ya biya ka.


A wannan matakin ne ake bukatar ka sayar da karfinka, da lokacinka, da iliminka, da basirarka don ka yi wa wani aiki shi kuma ya biya ka hakkinka. 


Kamar dai yadda ake yin aikin kwadago ko leburanci a zahiri, haka ake yi a yanar gizo. Mutane suna kwarewa a wasu fannoni wanda aikinsu kawai shi ne idan ana bukatar aikinsu a neme su a biya su su yi aikin.


Misalin irin ayyukan da ake yi sun hada da graphics design, web/app development, bug hunting, tutoring, content writing, advertisement, digital marketing, da sauransu. 


Akwai digital skills da dama da mutane suke kwarewa a kai kuma su zama freelancers su dogara-da-kansu. A makarantarmu ta Flowdiary Academy muna koyar da duk wadannan skills din.


3. Kasuwancin Kamasho

Sai hanya ta uku kuma ta karshe da ake samun kudi da ita a yanar gizo a karkashin online business ita ce kasuwancin kamasho wato affiliate marketing a turance. 


Wannan aikin ba shi da bambanci da aikin kamasho (commission) da ake yi a zahiranci. Misali, idan ka je hawa mota a tasha, za ka ga dan NURTW ya nema maka mota ya saka ka har a tashi, shi kuma daga baya sai direban ya sallame shi.


To aikin kamasho na nufin nema wa wani kamfani kwastomomi shi kuma ya ba ka wani abu wato kasonka (percentage.) Ana wannan sana'ar a yanar gizo kuma ba ta da matsala.


Wasu lokutan irin kamfanonin sayar da kayayyaki za su ce idan ka kawo musu duk mutum daya wanda ya yi sayayya a shafinsu za su ba ka kaso 3% cikin 100% na kudin da ya kashe, misali irin su kamfanin Amazon, BlueHost, Konga da sauransu.


Irin wannan kasuwancin ana yin shi ne musamman idan mutum yana da shafin yanar gizo (website/blog) inda mutane suke ziyarta.


A takaice, wadannan su ne hanyoyi guda 3 da ake samun halastaccen kudi da su a yanar gizo. Duk wata hanya da za a kawo ko sun kai 100 to a karkashin wadannan suke.


Amma a yanzu 'yan damfara suna amfani da duk wadannan hanyoyin su cuci mutane kuma su gurbata kalmar online business, sai ka ga mutum yana harkarsa ta bayan fage idan ka tambaye shi sai ya ce online business yake yi ashe ba hanyar da ta dace yake bi ba.


To a cikin wadannan hanyoyin guda uku hanyar da 'yan damfara suka fi yawaita a kai ita ce hanya ta uku, wato affiliating ko affiliate marketing. A wannan gabar za su ba ka link su ce idan ka yi register kuma ka yi investing bayan wasu kwanaki za a rubanya maka kudaden da ka zuba.


Dan'uwa duk wata hanya da za ka samu kudi a yanar gizo matukar ba ta cikin misalan da na kawo a sama ba, to gaskiya ba lallai ba ne ta kasance ingantacciya ba. 


Kada ka yi kokarin shiga harkar damfara ko kuma ka janyo wasu cikin ta. Don haka duk wanda zai ce maka yana online business matukar dai ta kirki ce to dole za ta kasance daga cikin misalan da na kawo a sama.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post