Ministan Sadarwa Ali Pantami Ya Nada Jarumi Nuhu Abdullahi Babban Mukami


Isa Ali Pantami Ministan sadarwa da tattalin arziki ya nada Nuhu Abdullahi matsayin jakadan Shaidar dan kasa karkashin Hukumar bayar da Shaidar Dan Kasa ta Najeriya (NIMC). 


Nuhu Abdullahi wand aka fi sani da Mahmoud a cikin shirin nan mai farin jini na dogon zango 'Labarina' ya bayyana murnar sa a yayin da ya wallafa hoton takardar da aka bashi mukamin. 


Sanarwar nadin na kunshe ne a cikin takarda da hukumar NIMC ta aika wa jarumin a makon  da ya gabata. Inda dubban jama'a suka dinga taya shi murna. 


A cikin ayyukan da zai gudanar a wannan matsayi shi ne jagorantar fadakarwa da wayar da kan jama’a kan muhimmancin mallakar shaidar dan kasa da tsare-tsaren gwamnati kan shaidar zama dan kasa da kuma alfanunsa.


Jarumin zai kuma halarci duk tarukan wayar da kai a bainar jama’a da hukumar ta shirya, da kuma ta kafofin yada labarai kan muhimmancin mallakar shaidar dan kasa, da sauran shirye-shiryen na fadakarwa.


Nadin na shekara guda ne, kuma ya soma aiki tun ranar 16 ga watan Satumba da muke ciki.


Abdullahi Nuhu ya dade yana fitowa a fina-finan Kannywood, kuma fin din da ya fara tashe shi ne shirin mai dogon zango na Labarina, a inda ya fito a Mahmoud.


Wanda yanzu kimanin aka daina ganin sa a cikin shirin na 'labarina'. Sai dai kuma wasu name bayyana hakan a dalilin samun sabani da suka samu da masu shirin Film din 'labarina'. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post