Kungiyar Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari A Masallachi Sun Kashe Masu Ibada Da Dama A Jihar BornoMayakan Boko Haram sun kai hari a wani Masallaci da ke jihar Borno ta Najeriya, inda suka kashe babban limamin Gima tare da karin wasu masu ibada.


Hakazalika harin wanda ya auku a ranar Juma’a, ya kuma raunata mutane da dama, yayin da ‘yan ta’addan suka mamaye garin Ngulde da ke Karamar Hukumar Askira -Uba ta jihar Bornon.


Mayakan da yawansu ya kai 20, sun kai farmakin ne a sanyin safiyar ranar ta Juma’a , inda suka yi ta bude wuta kan mutanen da suka kammala sallar Asuba a Masallacin.


Har ila yau, mayakan sun yi awon gaba da dabbobi da abinci, sannan suka cinna wa wasu motoci wuta a garin na Ngulde wanda ke kusa da dajin Sambisa.


Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare na kisan mutane babu kakkautawa a Najeriya duk da ikirarin gwamnatin kasar na samun galaba a kan mambobin kungiyar.


Ko a satin da ya gabata sai da wasu 'yan bindiga suka kai hari a wani Masallacin juma'a a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da masallata da dam. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post