Iman Abdulati Ahmad Matar Da Tafi Kowace Mace Kiba A Fadin Duniya


Iman Ahmad Abdulati, matar da ta fi kowacce mace kiba a duniya a shekarar 2016, sakamakon larurar kumburar da aka haife ta da ita.


Nauyin Iman, ’yar asalin kasar Masar ta kai kilogram 500, daidai da nauyin buhun shinkafa 10.


Ita ce mace mafi kiba a shekarar 2016, kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito.


Ita dai Iman Ahmad Abdulati ta rayu tana da shekaru 36, kuma ba ta bar gidanta da ke birnin Alexandria ba tsawon shekaru 25 kuma ba ta iya motsawa daga kan gadonta ko ma birgima saboda girman jikinta, inji rahoton Daily Mail. 


Ta dogara ga mahaifiyarta da 'yar uwarta Chaymaa Abdulati don yin ayyukan yau da kullum kamar cin abinci, canza tufafi, tsaftace inda take kwance. 


Kafin rasuwarta a watan satumbar 2017, sai da ta shekara 25 a kan gado, saboda kafafunta ba sa iya daukar nauyin jikinta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post