Idan kunaso kuyi nasara a rayuwarku ku guji Yin mu'amala da irin wadannan abokai shida


Yawancin lokaci mukan kasance da abokanai waɗanda suke taka rawa wajen samun nasarar mu ko akasin haka. A matsayin ku na mutanen da kuke da yawan buri na rayuwa kuma kukeson son cimma burinku, yana da kyau ku zaɓi irin abokanan da za kuyi mu'amala da su don tabbatar da kun cimma burinku.


Kada ku kasance tare da mutanen da ba su da wani buri mai kyau a zuciyar su. Idan kuka fahimci mutanen da kuke tare dasu basu da wasu halaye masu kyau to ku kaurace musu. Yin hakan, zaisa ku sanya iyaka ga mutanen da kuke hulɗa da su da basuda wani buri mai kyau. 


A cikin wannan takaitaccen rubutun, za ku karanta wasu daga cikin abokanai guda shida waɗanda dole ne ku guje su idan kuna son cimma burin ku a rayuwa.


1. Son Kuɗi

Waɗannan nau'ikan abokai sun yi imanin cewa dole sai anyi kuɗi ko ta wani hali, koda yaushe zuciyarsu tana fada musu cewa sai sun yi kudi ko ta wace hanya. 


Ya kamata ku nisanci nau'ikan abokai masu irin wannan buri don guje wa fadawa akidar su idan kuna son yin nasara. Domin irin wannan abokai ba irin wanda za'a zauna dasu bane idan har ana so ayi nasara.


2. Masu Amfani Da Kai Don Cimma Burinsu (Users)

Irin waɗannan abokai suna tare daku ne kawai don su biya wata bukatar kansu tare da ku saboda son kai. Suna nan don amfani da ku don ajandarsu. Ba za su amfanar daku ba ta kowace hanya ba sai don su yi amfani daku su biya bukatar su.


Yana da kyau a ku daina abota da irin waɗannan mutane domin babu wata nasara da za su kawo muku a rayuwar ku.


3. Masu Kwaikwayo (competitors)

Kwaikwayo abu ne mai kyau idan har wannan abin zai kawo muka cigaba da cinma burin ku, amma kwaikwayo don yin takara da su ba abu ne mai kyau ba. Wasu abokai suna son suna son Kwaikwayo da yin gasa da mutanen da suke tare dasu.


Wadannan mutane suna da dabi'un da ke tilasta musu kwatanta da kuma yin gasa da mutanen da ke kewaye da su ta kowane hali. 


Irin waɗannan mutanen suna da wasu halaye da suke jin sai sun yi gogayya ko ta wane hali da waɗanda ba sa'annnin su bane. Idan kuna tare da irin waɗannan abokai da ke da son Kwaikwayon wasu don su burge, ku yi nesa dasu.


4. Ragwayen Abokai (Lazy Friends)

Malalaci wani nau'in aboki ne da ya kamata ku gujewa. Su irin wannan abokai ba su yi imani da aiki mai wuyar gaske ba. 


Basu iya jure yin aiki mai wuya, a karamin lokaci kawai suke so suga sunyi nasara. Basa yin wani aiki da zai iya kaisu da yin nasara. Idan kuna tare dasu a koda yaushe suna rage muku karfin gwiwa wajen cimma nasarar ku.


5. Masu iskanci (Flirty ones)

Waɗannan abokai ne da suke son yin kwarkwasa da abokanka na kishiyar jinsi ko kuma abokin tarayya. Za su iya lalata dangantakarku ta dogon lokaci tare da abokanka, dangi, da abokin tarayya. 


Kuna buƙatar saita iyakoki a tsakanin irin waɗannan mutane, tabbatar da kun guje musu ta kowane hali, kuma ku gargaɗe su da su daina irin wannan hali.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post