Hisba A Jihar Zamfara Ta Kame Namiji Da Mace Suna Jima'i Cikin Mutane A Tashar GusauWasu mutum biyu mace da namiji da ake zargin su da aikata lalata a bainar jama'a a cikin tasha dake birnin Gusau na jihar Zamfara sun shiga hannun 'yan hisba.


Shafin BBC Hausa ya rawaito cewa ankama waɗanda ake zargin da laifin yin zina tsirara a cikin jama'a ba tare da jin kunyar mutanen dake a wajen ba. Wanda hakan yasa mutanen da lamarin ya faru kan idon su suka sanar da hukumar Hisba.


Tun da farko dai ance shi namijin shine ya kalubalanci macen kan ya fita rashin kunya, inda itama ta kalubale shi wanda hakan yasa suka aikata zina a cikin mutane domin su nunawa duniya cewa su basuda kunya.


BBC Hausa ta tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Kotun Shari'ar Musulunci ta Kankuri da ke garin Gusau domin yi musu hukunci daidai da laifin da suka aikata.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post