Dalilan Da Suka Jawo Shirin Izzar So Ya Samu Karbuwa A Fadin Duniya - Inji Lawan Ahmad


Ko kunsan cewa shirin "Izzar So" mai taken soyayya wanda ake yinsa a masana'antar Kannywood shine shirin film din Hausa da yafi karbuwa kuma akafi kallon sa a yanar gizo-gizo. 


Shi dai wannan shirin ya yadu sosai inda ake haska shi a tashar YouTube ta Bakori TV wanda a yanzu haka suke da mabiya fiye da dubu 950. Sannan kuma ana haska shirin a gidajen talabijin na arewacin Najeriya har da makota. 


An yi kiyasin cewa, a awa ashirin da hudu kashi daya na iya samun ‘yan kallo 400,000. Wanda kawo yanzu shirin yanzu yakai, kashi na 98 a YouTube.


Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma mai shirya shirin tare da bayar da umarni a shirin "Izzar So" , Ahmad Lawan ne ya bayyana dalilin da ya jawo shirin ya samu karbuwa a duniya.


Fitattun jaruman Kannywood Ali Nuhu, Ahamd Lawan, Aisha Najamu da Nana Izzar So sune suke taka rawar gani a cikin shirin.


Mista Lawan, a wata hira da PREMIUM TIMES ta yi da shi ya ce shirin ‘Izzar So’ ya ginu ne a kan koyarwar Musulunci da kuma tafarkin Annabi Muhammad (SAW).


“Fim din, Izzar So, nasara ce a gare ni. Ina tsammanin wannan babban abu ne domin yana da asali game da yadda musulmi na gaskiya ya kamata ya kasance a rayuwa da kuma rayuwarsa ta soyayya. Fim ne da ya sa mutane da yawa suka sake chanza tsarin rayuwar su.


“Mun shirya wannan shiri ne domin mu nunawa mutane yadda za su yi rayuwarsu kan tafarkin mai kyau da kuma yadda Annabi (SAW) ya koyar da mu. Mutane da yawa sun jinjina min akan wannan fim din.


“Sannan ina alfahari a dalilin shirin, ‘Izzar So; mutane biyu sun shiga musulunci. Mata biyu  sun fito ne daga Gombe inda suka nuna min su masoyan fim din ne kuma suna ganin ya kamata su zama Musulmai. Sun ce sun koyi abubuwa da yawa game da addinin Musulunci a fim din kuma suna son su zama Musulmi. Yanzu su Musulmai ne.”


Don haka wannan shirin na "Izzar So" yayi tasiri sosai ga al'umma domin ya samu karbuwa sosai a ciki da wajen Najeriya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post