Dalilai Biyar Da Yasa 'Yan Mata Ke Son Auren Dattijan Maza


Binciken ya nuna cewa mata suna son samari  kyawawa 'yan gayu, sai dai a wannan zamanin yawancin 'yan mata sun fi son kasancewa da dattijan maza fiye da samari. 


Yin bayani akan dalilan da yasa 'yan mata suka fi son dattijan maza zai dauki tsawon lokaci, amma duk da haka akwai wasu halayya na dattijan maza dake jawo hankalin 'yan mata su ji sunfi son kasancewa da su fiye da samari. 


Ba tare da mun tsawaita dogon rubutu ba ga wasu halaye guda biyar dake jawo 'yan mata su ji sun fi son auren dattijai fiye da samari. 


(1)  Sun San Abinda Ya Kamata Kuma Suna Da Hikima;

Zancen gaskiya duk mace tana son kasancewa da namiji wanda yasan abubuwan da suka dace da kuma kulawa akan ta. Suna son namijin da zai tsaya ya kula da su cikin aminci da amana. Manyan maza masu shekaru suna da Hikima da kuma kulawa tare da nuna gaskiya hakan yasa wasu matan ke son kasancewa da dattijon namiji. 


(2) Suna Sauke Dukkan Nauyin Dake Kansu;

Kamar yadda muka fada a sama dukkan wata mace na son yin tarayya da dattijon namiji wanda zai kula da ita ya biya mata bukatar ta musamman bukatun da suka shafi kudi. Tsofaffi suna da kulawa wajen biyawa mata bukatun su hakan yasa matan suka fi son kasancewa da su. 


(3) Dattijan Maza Basa Canja Ra'ayin Su;

Mata suna son kulawa da nuna musu soyayya a koda yaushe, hakan yasa suke son auren dattijai a maimakon samari, domin su samari sukan iya canja irin yadda suke nuna so ga macen da suke tare da ita. 


(4) Dattijai Basa Yin Wasa Da Hankalin Mata;

Tsofaffi basa yin wasa da hankalin mace, basa yin wasa da tunanin tanan domin su samu biyan bukatar kansu. Suna tsayawa akan gaskiya don tabbatar da sun kula da mace da ba ta hakkin da ya dace da ita. 


(5) Sun San Yadda Za Su Saka Mace Taji Dadi

Menene dangantaka mai kyau ba tare da jin dadin jima'i ba? Manya maza sun san abin da mata ke so a gado. Sun ga abubuwa da dama dake saka mace taji dadi, duk wasu hanyoyin da za su saka mace taji dadi ta gamsu sun sani sabanin samari. 


Wannan sune kadan daga cikin wasu dalilai guda biyar dake jawo mata su kamu da son dattijan maza fiye da samari. Sai dai idan kuna da wasu dalilan za ku iya bayyana mana su a kasan wannan rubutun. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

 1. Hmn Amma fa akwai ranar kin dillanci!
  Ko Yan mata sunsan cewa scientifically bincike ya tabbatar da
  #Menu_Pause? Yan matan da suke wannan gangancin sunsan shekara nawa ne na da namiji?
  Idan Tsohon da kika aura Yana Baki kulawa irin ta ma'amular kwanciya to Yana kaiwa Menu_Pause ya Daina sha'awa.
  Matsalar ba a shi ta tsaya ba ke Kuma a wannan lokacin kin Kai wasu shekaru da sha'awar ki ta nunku. Saboda bincike ya tabbatar da wasu shekaru da idan mace ta Kai sha'awarta nunkuwa take a wannan lokacin shi Kuma ya Daina SHA'AWA to ke Kuma ya za kiyi?
  Sai ki fara Neman Mazan banza kina yin Zina?
  Hmn! Yan mata adai kula saboda kuskuren ki na wannan gangancin zai lalata Gobenki
  Wannan shawara ce kyauta na Baki. Amma kuyi tunani Akai.
  @Bello Yusuf Ibrahim Gaya.

  ReplyDelete
Previous Post Next Post