Yajin aikin ASUU: Ɗan aji biyu a jami'a ya koma saida shayi da biredi da soya indomi a Kano


Wani dalibi mai matakin karatun digiri aji na 200 a Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) da ya koka kan yadda kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aikin ya bude wata sana’ar hadin gwiwa ta “siyar da shayi ” a garin Dawakin Dakata a yankin karamar hukumar Nassarawa Kano don gujewa zaman banza. 


Dalibin wanda yake a fannin nazarin tarihi da hulda da kasashen duniya wanda ya bayyana kansa a matsayin Yusuf Auwal Burkum ya ce ya yi nadamar rashin kafa sana’ar tun da farko.


Haɗin shayi, sana'a ce ta dafa abinci na gida, ana siyar da kwai, shayi da burodi, galibi a cikin sarari mai ƙaramin tanti, benci da kujeru.


Barkum ya ce muna da wurin zama muna hira, da yawa daga cikinmu za su sha shayi, yawancin kuma idan za'a siyo shayin sai sun  je wurare masu nisa sannan za su siya, ya ce...


Burkum ya ce daga baya ya yanke shawarar cewa zai iya bunkasa kasuwancin a kusa da wurin domin mutane su samu sau kin siya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post