Dattijo Dan Shekara 80 Ya Auri Zankadediyar Budurwa A Karon Farko Bayan Shafe Rayuwar Sa Ba Tare Da Aure Ba


Wani dattijo mai shekaru 74 dan asalin jihar Kogi mai suna Mallam Muhammad Auwal, ya yi aure a karon farko bayan shafe tsawon rayuwar sa bai yi aure ba. 


Malam Auwal ya auri wata budurwa ‘yar shekara 45, Mallama Rahmat Muhammad, a Lokoja, babban birnin jihar Kogi a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta.


Da yake magana da manema labarai kan dalilin da ya sa ya zauna a wannan tsawon lokacin ba tare da yai aure ba, Malam Auwal ya ce rashin kudi ne ya sa shi kasa yin aure da wuri.


"A koyaushe ina tsoron kada in gaza a wajen gudanar da aikina, hakan ne yasa ba zan iya kulawa da mace ba. Wanda kuma hakan babbar barazana ne, domin ana so ma'aurata su kula da junan su ni kuma aikina ba zai bari inyi hakan ba. 


Don kar na kasa kulawa da matar da zan aura yasa na kasa yin aure tun da wuri, don haka don guje wa wannan duka na yi watsi da maganar auren gaba daya, amma yanzu Allah ya sa hakan ya tabbata.

" Ko da ake tambayar sa cewa Ko a lokacin da yake matashi yana kula 'yan mata, sai ya ce; " eh lokacin yana kula 'yan mata amma ba da yawa ba saboda halin rashin kudi da yake fama dashi. Hakan yasa yawancinsu sun raina ni, galibi saboda talauci na. Amma na gode wa Allah a baya ne hakan ya faru." Akan abin da ya ja hankalin sa ga sabuwar matarsa ​​da ko zai tara yara da ita, sai ya ce; Allah ne kadai ya san ko za mu haihu, ba ka taba sanin abin da Ubangiji zai iya yi ba, ba a hannunmu yake ba, amma yana hannunsa.” 


A nata bangaren Rahmat tace Allah ya kaddara cewa za mu yi aure, kuma addu'a ta shine Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya da fahimtar juna a gidanmu." Ta kara da cewa inajin dadin auren mu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post