Bayan biyan kudin fansa har N500,000 ga 'yan bindiga sun karbe kudin kuma sun kashe mutumin


Wasu masu garkuwa da mutane sun harbe wani matashi dan shekara 32 da ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Moddibo Adama (MAU) da ke Yola a jihar Adamawa, bayan sun karbi kudin fansa naira N500,000 daga hannun iyayensa.


An yi garkuwa da Abdulmalik Tukur, wanda kwanan nan ya kammala shirin yi wa kasa hidima na kasa (NYSC) na shekara daya a jihar Plateau a gidansu da ke unguwar Vinkilang da ke wajen Yola tare da wasu mutane shida a daren Litinin.


Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa daga bisani, ƴan bindigar sun saki wadanda su kai garkuwar da su bayan an biya kudin fansa har Naira 400,000 ga kowannen su. Sai dai masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 a kan Abdulmalik.


Bayan an shafe kwanaki uku ana ciniki da su, an cimma matsaya da iyalan mamacin inda suka aika da wakili ya kai Naira 500,000 da aka amince da su a wani wuri a cikin dajin.


Wani dan uwan mamacin ya ce mahaifin Abdulmalik ya kai kudin ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Alhamis.


“Bayan sun kammala kirga kuɗin, sai suka saki Abdulmalik ya koma gida. Yayin da ya fara tafiya kawai sai suka harbe shi da bindiga ba tare da wani bayani ba,” inji shi.


Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, SP Sulaiman Nguroje, ya ce har yanzu bai samu rahoton faruwar lamarin ba. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post