Innalillahhi: Ƴan Bindiga Sun Yiwa Matashiya Mai Yiwa Ƙasa Hidima Fyaɗe


A ranar Talata ne wasu mutane da ake zaton ƴan bindiga ne suka kutsa kai cikin wajen kwanan masu yiwa kasa hidima dake kan hanyar Udo Ekong Ekwere a garin Uyo, Jahar Akwa Ibom, inda suka yiwa wata matashiya fyade sannan kuma suka sace kayan amfanin su da ya haɗa da kuɗaɗe da wayoyi da kuma na'urar kwamfuta.


Emeka Emmanuel, wanda daya ne daga cikin masu yiwa kasa hidima da abin ya faru kan Idanun sa yace maharan sun shigo gidan ne da manyan makamai inda suka fara haske su da fitilu suna tashin su daga bacci tare da yin barazanar kashe mu idan ba mu basu hadin kai ba.


Wata daga cikin masu yiwa ƙasa hidima da ta nemi a ɓoye sunan ta tace maharan ba su yi mata komai ba amma dai sun ƙwace mata wayar ta da kuma kwamfuta.


Ta Ƙara da cewa, ” Sun iske mu ba tare da shiri ba. sun haska fitila a tagar ɗakin tare da gargaɗin harbi idan ba’ayi saurin bude Ƙofar ba.


Wani daga cikin mazaunin yankin, Bossey Offiong, ya bayyana cewa ya kai rahoton ga hukumar Ƴan Sanda ta Iko Akpanabia wacce itace mafi kusa dasu, Amma basu halarci wurin ba har sai bayan da yan ta’addan suka tafi.


A lokacin da aka buƙaci jin ta bakin, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar, SP Odiko Macdon, ya bayyana cewa ” Bashi da wata masaniya dangane da faruwar lamarin, amma zan bincika, sannan in sanar daku “.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post