Anyi Bikin Baiwa Wani Kasurgumin Dan Ta'adda Sarauta A Zamfara Domin Dawo Da Zaman Lafiya A Jihar


Wani rahoto dake fitowa daga jihar Zamfara na tabbatar da cewa yawan 'yan ta'adda sun halarci bikin nadin sarauta ga kasurgumin dan bindiga Ado Aliero a matsayin Sarautar Sarkin Fulanin Yandoto. 


Tun da farko dai mahukunta a jihar sun haramta wannan muka in Amma dai haka aka yi shagalin bikin nadin ga Ado Aliero, cewar wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa. 


Amma dai ance a yayin nadin anga kwamishinan tsaro na jihar ta Zamfara da shugaban karamar hukumar Tsafe Ibrahim Mamman Tsafe. duk sun halarci bikin nadin Ado Aliero. 


Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa anyi wa Ado Aliero nadin sarautar ne sakamakon irin rawar da yake takawa wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin masarautar da kuma 'yan bindiga da suka addabi karamar hukumar Tsafe 


Majiyoyi daga fadar kuwa sun ce gwamnatin jihar ta yi umurnin dakatar da nadin ne bisa fargabar yadda al’umma za su dauki lamarin, bayan da wasu kafafen yada labarai suka bankado shirin.


Sai dai shugaban kwamitin kwance damarar 'yan bindiga a jihar Zamfara ya tabbatar wa da sashen Hausa na RFI cewa lallai an yi wannan nadi ne don a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar, duba da cewa babu wani zabi da ya wuce haka.


Yanzu dai gwamnatin jihar ta bayyana kamo mata Sarkin da ya baiwa Ado Aliero wannan sarautar, sannan kuma ita gwamnati ta haramta wannan nadin da aka yiwa Ado Aliero. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post