Ahmed Musa ya caccaki ‘yan siyasar Najeriya kan yadda suke tura 'ya'yan su karatu waje


Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa, ya caccaki ‘yan siyasar Najeriya kan yadda ba su damu da ilimi ba, yayin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aikin. Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan da hotuna suka mamaye yanar gizo yayin da Jordan Nyesom-Wike, dan Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya kammala digiri a Jami’ar Exeter, da ke Birtaniya.


Wadanda suka halarci bikin kammala karatun  Jordan da aka dauka a cikin hoto sun hada da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, matar Wike, Justice Eberechi Nyesom-Wike da diyar sa, Jasmine Nyesom-Wike. 


A halin da ake ciki dai, dalibai a Najeriya sun kasance a gida tun bayan da ASUU ta fara yajin aikin a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, yayin da JAC ta fara nata a ranar 14 ga Afrilu, 2022.


Kungiyoyin sun fara gudanar da yajin aikin ne  bayan da gwamnati ta kasa cika musu alkawarin da tai musu yayin da suka bukaci a inganta tsarin jin dadin ma'aikata, da kyautata yanayin aiki, da aiwatar da yarjejeniyoyin ma’aikata daban-daban da suka rattaba hannu da gwamnatin tarayya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020, inji rahoton Punch. 


Wannan ne ya tilastawa Ahmed Musa caccakar 'yan siyasar Najeriya bisa irin rikon da sukaiwa ilimi a kasar, haka kuma zargi matasa da cewa suma suna da nasu laifin da suke biyewa yan siyasar ba tare da sanin inda aka dosa ba.


“Ga ‘yan siyasar mu da ’ya’yansu ke karatu a kasashen waje, yaya kuke ji idan kuna ziyartar ‘ya’yanku a kasashen waje kuna daukar hotuna a makarantunsu kuna yadawa a yanar gizo yayin da ASUU ke yajin aiki? “Kamar seriously, yaya lafiya gareki.


Kuna gudanar da tsarin da ku kanku ba ku yarda da shi ba, ku nuna mini wani dan siyasa wanda yaron sa ke yin karatu a Najeriya.


A baya Jaridar Legit.ng ta rawaito cewa Musa ya ci gaba da tallafa wa al’ummarsa yayin da  ya ringa bayar da tallafin Naira 20,000 ga kowannensu ga mutane kusan dubu biyar a garin Jos. irin wannan adadin na Najeriya na kasa da kasa. Musa wanda ya shahara wajen taimaka wa gajiyayyu da marasa lafiya, ya yi wannan na baya-bayan nan ne a lokacin da ya mika kyautar kudin ga daidaikun mutane. 


Labari Daga: Jaridar Legit.ng

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post