Yanzu yanzu: ƴan ta'ada sunyi garkuwa da mahaifiyar A A Zaura a Kano

 

Wani rahoto dake fitowa ya bayyana cewa, ana zargin wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba, da sace mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim (A A Zaura), mai suna Hajiya Laure.


Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, an sace mahaifiyar dan siyasar ne da asubahin ranar Litinin kafin safiya, kamar yadda shugaban karamar hukumar Ungoggo, Abdullahi Garba Ramat, ya tabbatar da faruwar lamarin.


Ramat yace an sace Hajiya Laure ne a gidanta dake garin Zaura a mazabar Rangaza ta karamar hukumar Ungoggo, kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar masa.


Sai dai har kawo zuwa haɗa wannan rahoton ba'a san suwaye suka ɗauke Hajiya Laure ba. Kuma babu wani rahoto dake nuna cewa an kashe wani a yayin kai wannan harin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post