Birnin Lagos Ya Zama Birni Na Biyu A Duniya Mafi Ƙuncin Gudanar Da Rayuwa


A wannan makon ne aka fitar da wani bincike da masana tattalin arziki suke fitarwa a duk shekara, binciken na bana ya nuna birnin Lagos shine birni na biyu mafi munin gudanar da rayuwa a duniya, inji rahoton.


A rahoton da masanan suka fitar ya nuna birnin Damascus na ƙasar Syria shine birni na farko mafi matsanancin rayuwa a sakamakon yaƙi da ake fama dashi a yankin, wanda ko a bara ma kididdigar da aka fitar shine na farko.


Baya ga birane mafi munin rayuwa akwai kuma birane mafi kyawun rayuwa da suma ake fitar da kididdigar su. A halin da ake ciki, Vienna babban birnin kasar Austria ne ya sake darewa matsayin birni mafi kyawun rayuwa a duniya.


A shekarar bana rahoton kwararrun bai hada da Kyiv babban birnin Ukraine ba, bayan da Rasha ta mamaye kasar a karshen watan Fabrairu.


Masana tattalin arzikin na nazartar batutuwa da dama da suka hada da wadatar ababen more rayuwa, ingancin sufuri, kiwon lafiya, ilimi da kuma tsaro da kwanciyar hankali wajen tantance matsayin yankuna ko biranen duniya dangane da kyawun zamantakewar da mutane ke yi a cikinsu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post