An shiga shagulgulan bikin Jaruma Ummi Rahab da Mawaƙi Lilin Baba


Bayan tsawon lokaci da aka ɗauka ana ta raɗe-raɗi akan batun auren Jaruma Ummi Rahab da fitaccen Mawaƙi Lilin Baba a ƙarshe dai ta tabbata lokaci yazo.


Tun farkon shekarar 2022 ne dai labarai sukai ta yawo a kafafen sadarwa na zamani akan cewa za'ayi auren a watan Fabrairu. Ummi Rahab dai wacce take shirin zama amarya cikin wasu awanni masu zuwa jaruma ce a masana'antar Ƙannywood wacce tauraruwar ta ke haskawa a wannan lokacin. Wanda hakan yasa wasu da dama ke tunani cewa batun auren ta da Lilin Baba ba gaskiya bane.Sai dai kuma a ranar Alhamis ita dakanta Jarumar ta wallafa katin gayyata zuwa taron cin abinci da zarar angama ɗaura musu aure a ranar Asabar 18/6/ 2022 a Meena Even Center dake kan titin Lodge Road Nassarawa GRA Kano state.Shi kuma auren za'a ɗaura shi ne a Tudun Murtala Nepa Office hannu riga da gidan Bala Ƙasa misalin ƙarfe 11 na safe.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post