Yanzu-yanzu: Hukumar Shirya Jarabawar JAMB A Najeriya Ta Saki Sakamako


Hukumar dake shirya jarabawar shiga jami'a a Najeriya da akafi sani da JAMB ta sanar da fitar da sakamakon Jarabawar da ɗalibai suka zana a bana a faɗin ƙasa.


Fabian Benjamin shine shugaban sashen hulɗa da jama'a na hukumar ta JAMB, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Asabar, inji rahoton Jaridar The Nation. Inda ya bayyana cewa ɗaliban da suka samu zana jarabawar za su iya duba sakamakon su ta wayoyinsu na salulu.


"Don duba sakamakon UTME, kowane ɗalibi da ya rubuta Jarabawar zai iya duba abinda ya samu ta wannan hanyar kamar haka: tura UTMERESULT zuwa 55019 da lambar wayar da akayi amfani wajen rijista, za'a turo musu sakamakon su kai tsaye."


"Wannan shine hanya daya tilo da aka samar don duba sakamakon a yanzu don wasu dalilai." Don haka duk ɗalibin da yasan cewa ya zana jarabawar JAMB to yai gaggawar duba sakamakon sa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post