Sanata Ibrahim Shekarau Ya Bayyana Dalilan Da Yasa Ya Koma NNPP


Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar APC zuwa NNP, jam'iya mai kayan marmari. Da yake ganawa da manema labarai a Kano a ranar Laraba, Shekarau ya ce ya fice daga jam'iyyar APC ne saboda shugabancin jam’iyyar a jihar ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka na tafiya tare da shi da magoya bayansa a harkokin jam'iyar.


“Duk da irin gudunmawar da muka bayar, magoya bayan mu sun yi mamakin yadda a ke samun rashin yabawa da kuma rashin yi da mu a al'amuran jam'iyar.


“A matsayinmu na ‘yan jam’iyya masu kishin ƙasa kuma muna sane da ayyukan da muke da su a matsayinmu na mazauna jihar Kano, don baiwa gwamnati shawarwari da goyon bayan da ake buƙata don samun nasara, mun jajirce kuma muka ci gaba da lalubo hanyoyin da za mu tuntuɓi gwamnati.


"Amma abin takaici, duk wannan ƙoƙarin namu bai samu karɓuwa ba, ƙarshe ma sai ka ga an sace mana gwiwa. "Ganin hakan ne ya sanya mu ka yi duba na nutsuwa mu ka ga cewa wani yunƙuri ne da APC da gwamnati ke yi na ajiye mu a gefe da mu da magoya bayan mu," a cewar sa.


Shekarau ya ƙara da cewa ba'a gudanar da zaɓen shugabannin  jam’iyya na jiha bisa ka’idojin da aka gindaya ba. Wannan dalilan ne yasa muka fita daga wannan jam'iyyar muka koma NNPP, a cewar Shekaru. Ya kuma ce zai sake neman tsayawa takarar Sanata a jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023.


Shigar Sanata Malam Ibrahim Shekarau daga APC zuwa NNPP ya ƙara ɗaga jami'yar a Jihar Kano, inda wasu ke ganin cewa haɗewar sa da tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso a jam'iya guda zai kawo babbar nasara a zaɓen da za'a gudanar na 2023.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post