Ni Kaɗai Ne Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A Jam'iyyar APC A Zaɓen 2023 - Cewar Tinubu


Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce shi kaɗai ne ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da za'a gudanar a 2023.


Ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar APC a gidan gwamnatin Jihar Neja, gabanin zaɓen fidda-gwani da za a yi. Tinubu ya bayyana cewa ci gaban da ya samu a matsayinsa na tsohon gwamnan jihar Legas, tarihi ne cewa shi kaɗai ne zai iya ceto ƙasar nan daga halin da ta ke ciki.


“Ni kaɗai ne ke takarar shugabancin ƙasarmu mai girma, ban san inda wasu masu gudu za su je ba; Ni kaɗai ne nasan hanyar ci gaban ƙasa. “Ni ne na fi kowa zama wanda ya dace da takara saboda tarihi na, na ɗaga mutane da dama, tun daga kansiloli, ƴan majalisa, majalisar dattijai, wakilai da gwamnoni, amma duk da haka suna nuna min yatsa.


“Za mu haɗa hannu don sake gina Najeriya wacce mu ke buƙata, kada ku damu da su; Ni kaɗai ne a cikin tseren, ku biyo ni ba zan ɓatar da ku ba, ni kaɗai ne ke da ilimi da ƙwaƙwalwar da zan yi wa Najeriya tunani.


Ahmad Bola Tinubu dai ana ta raɗe-raɗin cewa bashida cikakkiyar lafiya da zai iya jan ragamar jagorancin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa. Sai dai yasha fitowa yana ƙaryata hakan inda yake cewa babu wata laruruwa dake damun sa. Inda yake cewa."Ina da ƙwarin gwiwa, na yi hakan a Legas kuma zan zame wa Nijeriya alheri," in ji shi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post