Karo Na Biyu Abdulmalik Tanko Ya Musanta Zargin Da Ake Yimasa Na Kashe Ɗalibar Sa Hanifah


Biyo bayan zaman kotun da ya gudana a ranar Litinin da ake yiwa wani malamin makaranta akan zargin sa da yin garkuwa da kashe ɗalibar sa ya sake musanta zargin inda yace bashi ne ya kashe ta ba.


A yayin zaman kotun ne dake zamanta a  sakatariyar Audu Bako wanda Alƙali Usman Na-Abba ke jagoranta. Sai dai bayan da Alaƙalin ya sake zayyano tuhume-tuhumen da ake yi akan Abdulmalik Tanko nan take ya musalta laifukan da ake zargin sa da aikatawa.


Wanda kuma tun a zaman kotun na farko da ya gabata ya bayyana cewa duk ya aikata laifukan da ake zargin sa da aikatawa. Amma kuma daga bisani yayi amai ya lashe yace bai aikata ba. Yace laifin da ya aikata shine yin garkuwa da yarinya sannan kuma ya ɓukaci kuɗin fansa Naira dubu 100,000.


Ya amsa laifin cewar ya sace Hanifa ya kai ta makarantarsa ya rufe ta, sai dai ya ce ba shi da tabbacin ko shi kaɗai ne mutumin da ya ganta bayan binne ta da ya yi.


“Ba ni da tabbacin ko ni ne mutum na ƙarshe da na ganta, saboda na yi magana da wani mutum game da ita. Amma ban kashe ta ba kuma ban ba ta guba ba. Na barta tana bacci amma ina dawowa sai na tarar da ita ta mutu.


Ita dai Hanifa Abubakar an sace ta ne tun a ranar 4 ga watan Disamba 2021, a kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya, wanda daga bisani aka gano malamin makarantarsu, Abdulmalik Tanko ne ya kashe ta bayan ya buƙaci kuɗin fansa miliyan shida a hannun iyayenta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post