Da Ɗumi-dumi: Ƙungiyar ASUU na shirin janye yajin aiki


Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa, ASUU, za ta iya janye yajin aikin da ta ke yi a ko wanne lokaci da ga yanzu, kamar yadda jaridar DAILY POST ta jiyo.


Wani mamban kungiyar da ya zanta da wakilin jaridar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a halin yanzu malaman jami'o'in da ke yajin aikin na tunanin janye yajin aikin na tsawon watanni uku.


A cewarsa, dakatarwar na iya zama na tsawon watanni uku kacal, yana mai cewa za a ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya a cikin wa’adin watanni ukun.


Ya ƙara da cewa gazawar gwamnati wajen biyan bukatun ASUU ɗin cikin watanni ukun zai haifar da yajin aikin sai-baba-ta-gani.


Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya roƙi ASUU da ta duba halin da ɗalibai ke ciki, ta janye yajin aikin.


Kungiyar ta fara yajin aikin gargadi ne a ranar 14 ga watan Fabrairu saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunta da aiwatar da wasu yarjejeniyoyin da ɓangarorin biyu suka kulla a baya.


A ranar Litinin 9 ga watan Mayu ne aka tsawaita matakin na masana'antar da wasu makwanni 12, wanda ake sa ran zai wuce ranar 9 ga watan Agusta.

Tushen labari

Daga Jaridar Daily Nigerian

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post