Ƴan Fashin Daji Sun Hallaka Mutane Fiye Da 40 A Jihar Zamfara


Ana cigaba da tattara bayanai akan harin da wasu ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bakura yankin Sabon garin Damri na jihar Zamfara. A yayin kai harin ne dai ƴan bindigar suka kashe mutane sama da 40 sannan kuma suka jikkata wasu da dama da ba'a bayyana yawansu ba. Sannan suka yi awon gaba da tarin dukiya, inji wani mazaunin garin.


A hirar su da gidan Jaridar BBC Hausa mutumin mai suna Muazu Damri, ya bayyana cewa cikin tsakar rana ne ƴan bindigar suka afkawa garin nasu, wanda hakan yasa mutane suka fara gudu suna ihun ɓarayi. Daga bisani kuma sai muka fara jin harbi ta ko ina.


Sai dai wata majiya ta bayyana cewa jami'an tsaro sun kawo ɗauki a yayin da maharan suke harbe-harbe, kuma sun samu nasarar ƙwato wasu daga cikin kayayyakin da ƴan bindigar suka sace a garin. Mazauna garin dai sun bayyana cewa tun bayan kawo musu harin haryanzu suna zaune cikin rashin kwanciyar hankali.


Sunce ƴan bindiga sunyi musu ɓarna sosai fiye da yadda ake tunani, sun kashe mutane da dama kuma sun sace dukiyoyin al'umma, sai da muka lissafa gawar mutane 48 wanda ƴan bindiga suka kashe, a cewar Muazu Damri. Amma ya bayyana cewa mahukunta sun ɗauki mataki domin an turo da jami'an soji domin dawo da zaman lafiya a garin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post