Jihohi 7 Ne Kaɗai Suke Da Tsafta a Najeriya Ragowar 29 Duk Ƙazamai Ne – BincikeWani bincike da ƙungiyar 'National Technical Study Group For Nation’s Cleanliness' ta gudanar ta gano cewar jihohi 7 ne kaɗai ke da tsafta a cikin jihohin Najeriya, sauran 29 ɗin duk ƙazamai ne, a cewar rahoton. 


Binciken ya ce, jihohin Abuja, Kaduna, Bauchi, Legas, Akwa-Ibom, Cross Rivers da Ebonyi ne kawai ke da tsafta a cikin jihohin Najeriya 36.


Rahoton ya bayyana cewar, akwai takaici matuƙa yadda Najeriya ta zarta ƙasashen Chaina da India da suka nin ka ta yawan al'umma, wajen rashin tsafta.


Wannan yake nuna cewa kaso 80% na yankunan jihohin Najeriya basuda tsaftar mahalli. 


Daga ƙarshe ƙungiyar ta bayar da shawarar ɗaukar matakin da ya dace akan lamarin domin bunkasa tsaftace sauran jihohin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post