Siffofin Mutane Masu Jin Tsoron Allah


Ya ku bayin Allah! Ya kamata mu san siffofin masu tsoron Allah, domin mu yi qoqari mu yi koyi da su. Kadan daga cikin siffofin masu jin tsoran Allah, sune wadan da suke fadar gaskiya a kowanne hali, Allah yana cewa,


KARANTA: Siffofin Da Suke Hana A Auri Mace

KARANTA: Illolin kallon fina-finan batsa

KARANTA: Illolin dake faruwa da Budurwar da ta bari Saurayin ta yai zina da ita


(وَالَّذِي جَاءَ بِالصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِ أُولَئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ33) [الزمر: 33]


( Wanda kuwa ya zo da gaskiya kuma ya gaskata ta, wadannan su ne masu tsoron Allah”). 


muminai sune masu jin tsoran Allah, domin sune suke kiyaye abinda zasu furta, Allah madaukakin sarki yana cewa


(إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آَمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ ثُمَّ لَمْ يَرْتَابُوا وَجَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنْفُسِهِمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ15) [الحجرات: 15]


(Haqiqa ba wasu ba ne muminai sai wadanda suka ba da gaskiya da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi kokwanto ba, suka kuma yi yaqi da dukiyoyinsu da rayukansu a cikin hanyar Allah, wadannan su ne masu gaskiya).


masu fadar gaskiya sune masu jin tsoran Allah, kuma sune wadanda Allah yake gafarta musu zunubansu, Allah yana cewa 


يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا


(Yaku wandanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma ku fadi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma).


Yaku bayin Allah, dukkan wanda yake san Allah ya yarda dashi, to ya kiyaye dokokin Allah, kuma ya zama mai gaskiya, domin Allah yana cewa  


(قَالَ اللَّهُ هَذَا يَوْمُ يَنْفَعُ الصَّادِقِينَ صِدْقُهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ) [المائدة: 119]


(Allah yace, «Wannan ita ce ranar da masu gaskiya, gaskiyarsu za ta amfane su, suna kuma da aljannatai wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da Allah. Wannan shi ne babban rabo).


Don haka gaskiya ce take tseratar da bawa daga azabar Allah a ranar alqiyama.


 

Ya bayin Allah! Gaskiya na da matuqar amfani, a duniya da lahira, daga cikin amfaninta sun hadar da:


Na farko shigar da mai yinta gidan aljanna. An tambayin Annabi, (ﷺ), *menene aikin ‘yan aljanna? Sai ya ce, “Gaskiya”.Iman Ahmad ne ya rawaito shi.


Na biyu kubutar da mai yin ta daga halaka. Ya zo a cikin hadisin mutanen nan da dutse ya toshe musu qofar kogon da suka shiga cewa dayansu, ya ce da su, *“Babu abin da zai tseratar da ku sai gaskiya, kowannenku ya roqi Allah da abin da ya san yayi gaskiya a cikinsa.* Bukhari ne ya rawaito shi.


Na uku, "nagartar zuciya," duk wanda ya yi gaskiya a ayyukansa na fili to tabbas kuwa zuciyarsa na cike da gaskiyar nufi, domin kuwa komai bawa zai yi, to sai nufi ya rigaye shi.


Na hudu, gadarwa da mai yinta nutsuwa da kwanciyar rai.


Na biyar, *kubutar da mai yinta daga afkawa cikin fitintinun rayuwa.*


Na shida, "takan zama ga mai yinta, tushen aikata ayyukan alheri." 


Na bakwai, "korewa mai yinta siffantuwa da munafurci." 


Na takwas, "datar da mai yin a wajen hasashe da hangen nesa."


Na tara, "qarfafar hujjar mai riqo da ita da kuma yinta." 


Na goma, "samun yabo da kirari da kyakkyawan ambato daga mutane." 


Na sha daya, "jawo albarkar kasuwanci da san’o’i." 


Allah ka sa mu a cikin bayinka masu gaskiya, kuma ka tsare mu daga yin qarya da biyewa masu yinta amin."الله تعالى أعلم"_"ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​"Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post