Yanzu-Yanzu, Boko Haram sunyi Yunkurin Karbe sansanin Sojin Sama da ke Kaduna


Kungiyar Boko Haram, kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama, ta yi kokarin karbe sansanin sojojin saman Najeriya da ke Kaduna a safiyar ranar Asabar, kamar yadda Jaridar FIJ ta wallafa a shafin ta. 


KARANTA: Yan Bindiga Sunkai hari Barikin Soja sunyi awon gaba da garken Shanu
Wani jami'in rundunar sojan sama ya fadawa Jaridar ta FIJ cewa daga karfe 6 na safiyar Asabar, musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da jami'an soji wanda ya dauki kusan awanni biyu yana gudana.


 'Yan ta'addar sun kai wa sansanin hari ne ta bangaren baya. Inda Sansanin Sojan Sama yake, wanda yake babban waje ne, yana da saukin kasancewa mai rauni.


Wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da makiyaya suka je wani barikin Sojojin Najeriya da ke Jaji, Kaduna, suka sace shanu. Sai dai kuma ba a tabbatar da ko akwai asarar rayuka ba, amma an dade ana harbe-harbe a lokacin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post