Yadda Ƴan bindiga suka kashe ƴan sanda huɗu a jihar ZamfaraA jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda hudu.
 

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a yayin wata arangama da ‘yan bindiga lokacin da suke aikin sintiri a yankin Rini cikin karamar hukumar Bakura.


Haka kuma ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan Tataka da Takalmawa a karamar hukumar Zurmi inda ake fargabar fiye da mutum 20 sun mutu tare da kwashe ɗumbin dukiya a karshen makon da ya wuce .


A yan kwanakinna dai Hare-haren 'yan bindiga sun dawo sosai a jihar Zamfara. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post