MESSI YA SAYAR DA TAKALMIN SA A KAN KUDI DALA 175,000Lionel Messi: An yi gwanjon takalman dan ƙwallon ƙafar na Barcelona akan zun-zurutun kudi dala 175,000.

.Karanta: Cristiano Ronaldo zaiyi zaman jinya

An sayar da takalman Lionel Messi guda biyu don bada taimako akan kudi dala 175,000, inji Christie ya fada a ranar Juma'a.


Karanta karin bayani :An tsayar da buga wasan Premier League don a bawa dan wasa musulmi damar yin bude baki


Christie yace "An bayar da takalmin ne a gwanjon domin samun kudi don taimakon shirin kere-kere da kiwon lafiya na asibitin Jami'ar Vall d'Hebron dake Spain.Takalmin na Messi da aka sayar a ranar Juma'a shi ne ya saka lokacin da ya ci wa Barcelona ƙwallo ta 644 inda ya zarta Pele.
Messi ya karya tarihin Pele a matsayin wanda ya fi yawan cin ƙwallo a raga a ƙungiya ɗaya.


Pele, wanda ake wa kallon daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa, ya ci wa Santos kwallaye 643 tsakanin 1956 da 1974.

Kwallon da Messi ya ci wa Barca ya wuce kaka 17

Dan wasan gaba na Jamus Gerd Muller ya zo kusa da dacewa da Pele na zura kwallo daya a raga. Ya zura kwallaye 565 a kungiyar Bayern Munich tsakanin 1964 da 1979.

Fernando Peyroteo shine na gaba a jerin wadanda suka fi kowa yawan kwallaye bayan ya zira kwallaye 544 ga Sporting CP tsakanin 1937-49. Josef Bican shine na gaba da kwallaye 534 a Slavia Prague.
Messi, wanda ya fara taka leda a shekarar 2004, ya lashe kofunan La liga 10 da kuma Kofin Zakarun Turai hudu tare da kungiyar ta Kataloniya. Ya zura kwallon sa ta farko a shekara ta 2005.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post