Lokacin da ake karbar Adduar musulmi a ranar Juma'a


LOKACIN KARBAR ADDU'A A RANAR JUMA'A


Manzon Allah SAW yace:"A (Ranar) Juma'a a kwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace da shi, yana a tsaye yana sallah, sai ya rok'i Allah wani alkhairi face Allah ya bashi". Bukhary da Muslim. 

KARANTA: Shin zamu iya yin jima’i da daddare muyi wanka kafin muyi sahur?

KARANTA: Falalar yin sammako zuwa sallah juma'a


Abin da a ke nufi da "Yana tsaye yana sallah" ai yana zaune yana jiran sallah, yana ambaton Allah kuma yana addu'a, domin wanda ya zauna a masallaci yana jiran sallah to yana cikin sallah ne".


Shaykh Bn Bazz RA yace:


"Wannan lokacin shine bayan sallar la'asar har zuwa faduwar rana ga wanda ya zauna yana jiran sallar magriba, a masallaci ne ko a gida, mace ne ko namiji ya zauna yana jiran lokacin amsar addu'a, sai dai namiji ba zai yi sallar magriba a gida ba ko ma sauran salloli(na farillah) face da wani uzuri da Shari'a ta yarda dashi..."Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post