An gargadi mata da su daina aske gashin gaban su, domin hakan yana jawo matsala ta kiwon lafiya


Likita ta gargadi mata masu yawan aske gashin gaban su, su rika bada tazara domin kiwon lafiyar su


A wani rahoto da jaridar Nation ta wallafa ranar Alhamis, wata likita da ta kware a harkar lafiyar mata musamman wanda ya shafi gaban su, ta gargade su su daina aske gashin gaban su, cewa yin haka na da illa matuka.

Likitar mai suna Dakta Jen Gunter ta gargadi mata cewa aske gashin gaba na hadassa cututtuka kamar su kanjamau, ciwon sanyi, kurarraji da sauran su.

Likita Jen ta ce aske gashin gaba na iya hana mace jin dadin jima’i saboda gashin gaba na hade da jijiyoyin dake taimaka wa mace samun gamsuwa a lokacin jima’i.

Ta kuma ce rashin aske gashin gaba na taimakawa wajen hana iska mai sanyi shiga jikin mace.
Dalilin da ya sa mata ke aske gashin gaban su


Sakamakon binciken da aka gudanar akan mata 3,000 a kasar Amurka ya nuna cewa kashi 31.5% sun ce sukan aske gashin gaban su ne saboda gabansu ya fi kyan gani.

Wadannan mata sun ce hakan ya fi dacewa da su kamar yadda suke gani a fina-finan batsa da hotunan kyawawan mata a jaridu.

Daga nan kuma kashi 21.1% sun ce suna aske gashin gaban su ne saboda mazan su sun fi son haka.

Sun kuma ce sun fi aske gaban su yayin da za su sadu da mazan su domin burge mazan.

Sannan kashi 45.7% sun ce sukan aske gashin gaban su ne domin guje wa samun kwar-kwatar gaba.

Sun ce rashin aske gaba kazanta ne kuma yana sa gaban mace ya rika wari.

Hanyoyin da mace za ta iya kula da gashin gabanta.


1. Mace za ta iya rage gashin gabanta amma ba ta asked shi duka ba.

2. Tsaftace jiki da yin tsarki bayan an yi amfani da ban daki na taimakawa wajen kare mace daga kamuwa da cututtuka da kwar-kwatar gaba.

3. Sannan idan har ya kama a yi askin a tabbatar an bada ratan ranaku kafin mace ta sadu mijinta.
Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post