WANDA YAI SALLAR DARE SHI DA MATAR SA ADDUAR ANNABI ZATA SAME SU




WANDA YA YI TSAYUWAN  DARE  (SALLAN DARE) SHI DA  MATAR SA ADDU'AR ANNABI ZATA SAME SA


عن أبي هريرة قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم رحم الله رجلاً قام من الليل فصلى وأيقظ امرأته فإن أبت نضح في وجهها الماء رحم الله امرأة قامت من الليل فصلت وأيقظت زوحها فإن أبى نصحت في وجهه الماء.


Daga Sahabi Abi Huraira (R) ya ce, Manzon Allah (saw) ya ce, Allah ya jik'an mutumin da ya tashi cikin dare, ya yi Sallah, kuma ya tashi matarshi, idan tak'i se ya yayyafa ruwa a fuskarta.  Allah ya jik'an matar da ta tashi cikin dare zata yi Sallah, ta tashi mijinta idan yak'i se ta yi yayyafi ruwa akan fiskarsa.


Imam Abu Daawud ya ruwaito, kuma Albaniy ya ingantashi, Dariqus-salihin (61,pg)


Karin bayani:

  • Ba 'karamin rashi bane ace magidanta basu ta6a yin aiki da wannan hadisi ba.
  • Sannan ma'auratan da suke aiki da wannan hadisi zasu rik'a raya gidan su, da samun farin ciki da annushuwa.
  • Sannan mata, idan mijin ki bai san wannan hadisi ba, kada kiyi saurin fara yayyafa masa ruwa rana guda, a'a ku zauna cikin fahimta ki sanar masa da wannan hadisi da irin Addu'a da Annabi (SAW) ya yi ma wanda suka yi hakan. Ko da kin yi mishi hakan bazai zarge ki ba se dai ma ya ji daɗi domin ya dace da macen kirki..


Allah Ta'ala ya bada ikon aikatawa



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post