WANDA YA SHA AZUMI SAKAMAKON RASHIN LAFIYA BA ZAI CIYAR BA


WANDA YA SHA AZUMI SABODA RASHIN LAFIYA, BA ZAI CIYAR BA 


Tambaya

Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuh! 

 Malam A bani shawara:

 Na kamu da wata cuta ta zubar da yawu wanda bana iya kai azumi, yau shekara uku kenan, nasha azumi 23 da farko, shekara ta zagayo ban samu sauki ba na kuma shan 20 kuma ina tsoron kada wata shekaran ta riskeni shine na auno masara mudan nabi 43 akan akwai makwabtanmu yaran marayu ne, shin idan na basu na biya azumi na kokuwa? Nagode. 


Amsa

Wa'alaikumus Salam warahmatullah wabarakatuh! 

Idan har akwai tabbacin ciwon ba zai warke ba ka rama azumin, kana iya ciyarwa.

Amma in har akwai tunanin za ka warke to ba za ka ciyar ba, saboda wajibi akan mara lafiyan da ya sha azumi saboda lalura ya rama a wasu kwanakin na daban kamar yadda  Allah yake cewa: "Kuma wanda ya kasance mara lafiya bai azumci Ramdana ba, to ya rama abin da ya sha a kwanaki na daban" Suratu Al-bakarah aya ta:(185).


Aya ta (184) a cikin surar ta nuna wanda  ya sha azumi saboda rashin lafiya ko tsufa kuma babu tunanin ya samu damar ramawa nan gaba zai iya ciyarwa.


A bisa abin da ya gabata In har likita ya tabbatar za ka samu damar ramawa nan gaba to azumin yana nan a kanka, ciyarwa ba za ta wadatar maka ba.


Sannan in har ciyarwa ce ta halatta akanka ai ba mudun-nabi ake bayarwa ba !!!


Allah ne mafi sani 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post