DUK MUSLIMIN DA ZAIYI SALLAH NAFILA RAKA'A 12 A RANA SAI ALLAH YA GINA MASA GIDA A ALJANNAH



FALALAR KIYAYEWA GA NAFILFILI JERARRU


Daga Ummu Habiba matar Annabi (SAW) tace; Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su k'ara tabbata a gare shi yana cewa: "Babu wani Bawa musulmi da zai yi Sallah ga Allah a kowace rana raka'a goma sha biyu (12) na nafila bana farillah ba face sai Allah ya gina masa wani gida a Aljannah, ko kuma se an gina masa wani gida a cikin  Aljannah, Ummu Habiba tace ban gushe ba ina Sallatan su bayan wannan.


Muslim, cikin littafin Dariqus-Salihin


Wad'annan nafilfili jerarru (Rawaatib)sune, hudu kafin Azzuhar, biyu bayan Azzuhar, biyu bayan Magrib, biyu bayan Isha'i, biyu kuma sune raka'a biyu da ake yi kafin Asuba.


Mu Sani ba wanda zai cika farillai, ya kuma dage da nafilfili face se ya samu soyayya gurin Allah.

Allah ya bamu ikon kiyaye su tare da kyakkyawan niya da Ikhlasi (Amin)



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post