A CIKIN KWANA 4 KU MIKA WUYA KO KU FUSKANCI FUSHIN GWAMNATI, MATAWALLE GA YAN BINDIGA

 CIKIN KWANAKI 4 KU MIKA WUYA KO KU FUSKANCI FUSHIN GWAMNATI, GARGADIN DA MATAWALLE YAIWA YAN BINDIGA. 


Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya zargi wasu 'yan bindiga da yaudara gwamnati

Gwamnan ya ce ya samar da wata sabuwar dabara ta tsaro domin kiyaye mazauna yankin

'Yan bindiga sun mamaye wasu garuruwa a jihar ta Zamfara tare da hallaka mutane da dama

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargadi 'yan bindiga a jihar da su tuba ko kuma su fuskanci mummunan mataki daga gwamnati.

Gwamnan a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya tsara sabuwar taswira a yadda yake tunkarar matsalar tsaro da ke addabar jihar, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Yusuf Gusau, Channels TV ta ruwaito.

Matawalle ya bayyana cewa dakatarwar da aka yiwa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda hada kai da 'yan bindiga yana daya daga cikin sabbin matakan da ya yanke shawarar aiwatarwa.


Ya sha alwashin cewa nan da kwanaki hudu masu zuwa, zai shawo kan matsalar 'yan bindiga da ke damun mazauna a Jihar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post