FALALAR HAIHUWAR YA'YA MATA DA TARBIYARSU


FALALAR HAIHUWAR YA'YA MATA DA TARBIYARSU 


 Haihuwa ni'ima ce babba daga cikin ni'momin Allah mai girma, wacce ba kowa bane Allah yake masa baiwarta, hakan yasa Allah ya kasa mutane kashi hudu gameda wannan baiwar tasa;

1. Wani Allah ya bashi baiwa ta haihuwar ya'ya mata zallah.

2. Wani kuma Allah ya bashi baiwar haihuwar ya'ya maza zallah.

3. Wani kuma Allah ya haɗa masa maza da mata.

4. Wani kuma Allah ya jarrabeshi da rashin haihuwar gabaɗaya.

    Wannan rabe-raben mutanen gameda haihuwa Allah ya ambaceshi acikin Alqur'ani surah Ash-Shurah inda yake cewa {Ga Allah ne kaɗai mulkin sammai da ƙassai suke, yana halitta abunda yaga dama, yana bayar da kyautar ya'ya mata ga wanda yaga dama, wani kuma ya bashi ya'ya maza ya haɗawa wanda yaga dama kuma ya'ya maza da mata, sannan yasa wanda yaga dama ya zama fakara (mara haihuwa)} 

سورة الشورى ٤٩-٥٠

Wannan ayoyin suna ƙara tabbatar mana da cewa haihuwa ni'ima ce da ba kowa ke samunta ba, hakan yasa wajibine mutum ya godewa Allah akan wannan ni'imar matukan yanason rahamar Allah, domin butulcewa ni'imar Allah yana gadarwa mutum azabar Allah, kamar yadda Allah ya fada {Lalle ubangijinku ya shelanta muku cewa Haƙiƙa idan kuka gode zan ƙara muku, amma idan kuka kafurce kuka butulcewa Ni'ima ta to lalle azabata tanada tsanani}

سورة إبراهيم ٧.

Dan haka ya kai dan uwa ka kasance mai godewa Allah abisa kowane hali ka kasance acikin waɗancan rabe-rabe guda hudun can, hakan ne zaisa ka samu rabauta a wurin Allah.


  FALALAR HAIHUWAR YA'YA MATA

   Tabbas ya'ya mata ni'ima ce mafi girma, kuma rahama ce ga iyayensu, musulunci yazo da busharori masu yawa ga wanda aka haifa masa ya'ya mata wanda mai ya'ya maza bai samesu ba, ya'ya mata budi ne na samun Aljannah amma kaɗai ga wanda bai munanta mu'amala garesu ba, bai ƙyamacesu ba, baiji haushin haifa masa suba, matuƙar mutum yaji haushi a lokacin da aka haifa masa su koma ya ƙauracewa mahaifiyarsu ya zargeta dan ta haifa masa ya'ya mata to lalle akwai barazana mai tsanani akan wannan kuma waɗannan ya'ya matan zasu zama masa sanadiyar halaka matuƙar bai tuba ba. 


  Adarasi na gaba zamu kawo hadisai da suka yiwa magana akan falala da girman ladan wanda aka haifa masa ya'ya mata in sha Allah. Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post