YIN BACCI DA ALWALA SABABI NE DAGA CIKIN SABUBBAN AMSA ADDU'A

 


YIN BACCI DA ALWALA SABABI NE DAGA CIKIN SABUBBAN AMSA ADDU'A


Daga Sahabi Mu'az bn Jabal (Radhiyallahu anhu) Manzon Allah (SAW) yace; Babu wani mutum Musulmi da zai kwanta da ambaton Allah kuma ya kwanta da alwala kuma ya motsa (farka) a cikin dare, kuma ya roki Allah daga cikin alkhairan duniya da lahira face Allah ya bashi.


     -Abu Dawud ya ruwaito, kuma Al-baniy ya ingantashi


Karin bayani :

• Wannan falala ne na masu yin alwala yayin kwanciya bacci.


• Abinda ake nufi da ya kwanta da ambaton Allah, malamai suka ce ai ana nufin (ya kiyaye ya yi zikirorin kwanciya bacci).


• Don haka, duk lokacin daka kiyaye zikirorin (Addu'o'in) kwanciya bacci ka kuma kwanta da alwala, ka farka cikin dare ka roki Allah wani alkhairi zai amsa maka.


Allah Ta'ala ya sanya mu cikin wadanda zasu rika dacewa da wannan garabasa.

 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post