FALALAN ZUWA SALLAN JUMA'A DA WURI


FALALAN ZUWA SALLAN JUMA'A DA WURI


Daga Sahabi Abi Huraira R.A 


 Manzon Allah (SAW) yace;  "Idan ranar juma'a tazo, Mala'aiku suna tsayawa akan kofar masallaci suna rubuta na farkon zuwa da mai bin shi, kwatankwacin Wanda ya yi sammako, kamar kwatankwacin Wanda ya bada sadakan Rakumi, Sannan kamar Wanda ya bada Saniya, sannan Wanda ya bada Rago, sannan (kwatankwacin Wanda) ya bada Kaza, se Wanda kamar sun bada sadakan Kwai, Idan Liman yazo se su nad'e takardunsu, se suje su saurari Khuduba. -Bukhari da Muslim suka ruwaito, (Dariqus-salihin 77pg)


Karin bayani:

●Dukkanin wannan falalan (kwatankwacin ladan) za'a bada ne ga Wanda yaje kafin Liman yaje ne. Iya sammakan ka iya shagalinka.


●Idan Liman ya fara Khuduba, ba'a magana, ba'a cewa wani ya yi shiru idan yana yi. Ba'a wasanni (latsa) waya Ds.. Wanda ya aikata hakan ba shi da juma'a (falalan da ake samu na sallan juma'a).

Kadai ana yin shiru a dakatar da komai a saurari Hud'uba


Allah Ta'ala ya temake mu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post