WARIN BAKI WANDA A TURANCE AKE KIRA DA SUNA 'HALITOSIS'.


Warin baki cuta ce dake iya kama kowa, sai dai ance babu wata cuta da ba'a iya magance ta. 

Da yawa daga cikin mutane masu fama da warin baki, shiga cikin abokai ko 'yan uwa Yana yi musu wahala, sanadiyyar Janyo musu tsoron jin kunya ko kuma suna magna ana toshe hanci. 

Mutane da dama suna fama da wannan larurar musamman wadanda basa kula da lafiyar hakoransu da bakinsu. Amma duk da haka, wasu lokuta mutane sukan yi korafin cewa suna wanke bakin amma suna jin bakin su yana wari. To a gaskiyar magana duk masu irin wannnan ya kamata su ziyarci liktan hakori domin karbar shawarwari daga likitocin hakora domin tabbatar da lafiya da tsaftar hakora. 


Abubuwan dake kawo warin baki musamman idan ba'a wanke hakoran sune Kamar haka;


(1) Local factors;

Wannnan abubuwan sun kunshi; poor oral hygiene (wato rashin kula da tsaftar baki), shan taba sigari, kogon hakora, (dental caries/cavity) kurji a cikin baki, mouth ulcer da sauran su. 

(2) Certain foods or drinks;

Su wadannan sun hada da; yawan cin albasa, cin tafarnuwa, shan giya, cin goro da sauran abubuwa maka-mancin su. 

Warin baki dake da alaka da lafiyar dan adam, su wannan sun hada da;

 • Binkice ya nuna akwai ciwon cikin da yake haddasa warin baki. 
 • Ciwon sugar(Diabetes) 
 • Rashin isassun yawu a cikin baki
 • Ciwon dasashi har ya rika fitar da jini
 • Mura da tari mai tsananin gaske, wanda a turance ake Kira da pneumonia. 
 • Hepatitis
 • Magunguna; akwai magungunan da amfani dasu sukan janyo warin baki ta hanyar takaita gudanar yawun baka
 • Rashin cin abinci; idan aka kula da hakan idan akayi duba da yadda bakunan mu sukeyin wari a lokacin da muke yin azumi. 


Hanyoyin magance matsalar warin baki 

Hanyoyin da mutum zaibi domin ya kare kansa daga kamuwa da warin baki don magance matsalar sun hada da

 1. Wanke baki sau biyu a rana; wato mutum yai brush safe da yamma bayan angama cin abinci sannan kuma kafin a kwanta bacci shima ayi. Yawancinmu mun dauka cewa ana yin brush ne kafin a karya da safe, a'a anaso ne ayi bayan anci abincin safe, da kuma bayan anci na dare kafin a kwanta bacci. 
 2. Sauya brush ko asuwaki duk bayan wata biyu ko uku.
 3. Tabbatar da tsaftar abinci kafin a sanya a baki
 4. Yawan shan ruwa; hakan zai taimaka wajen Kara yawan yawu a cikin baki
 5. Kauracewa shan kayan zaki irin su chocolate, biscuits da sauran su kafin kwanciyar bacci. 
 6. Lazimtar kurkurar baki lokaci bayan lokaci da duma-man ruwa mai gishiri a cikin sa. 
 7. Cin kalolin abincin da ake Kira da 'self cleansing foods'. Su irin wadannan abinci sunada fibre a jikinsu, wannnan fibre yana taimakawa wajen automatic tooth cleaning. Irin wadannan abinci sun hada da; lemo(orange), rake(sugarcane), carrot da sauran su. 
 8. Ziyartar likitan hakori duk bayan wata shida domin yin wankin hakora, hakan zai taimaka wajen fidda duk wani abincin da ya makale jikin hakora wanda brush bazai iya fiddawa ba. 

Abubuwan da ya kamata mu fahimta game da warin baki, duk yadda mutum yake kula da bakinsa wurin tsaftace shi (yin brush/asuwaki) bazai hana bakin yayi wari ba idan har ya kasance;

 • Ba'a wanke ko'ina cikin baki: Anaso a lokacin wanke baki a wanke ko'ina, wato ciki da wajen hakora, mataunan hakora. Sannan yanada matukar muhimmanci a wanke harshe a hankali. Da yawan mu mukan dauka cewa harshe baya bukatar wanki idan har mun wanke hakoran mu, wanda hakan ba haka yake ba. Harshe yanada bukatar tsaftacewa shima. 
 • Idan ya kasance akwai kogo/ rami a hakori/hakora, Sannan ba aje asibiti domin ganin an cike shi ko an cire shi ba(idan bukatar hakan ta taso). Barin kogo a jikin hakori yana sawa abinci ya rika taruwa a cikin rami/kogo har ya rika haifar da warin baki. 
 • Duk yadda akaso ayi maganin warin baki Indai ana yawan cin nau'in abincin dake sa warin bakin Kamar su albasa, tafarnuwa da-dai sauran su, to zaiyi wahala a iya magance matsalar kai tsaye.
Sannan yana da kyau musani cewa;
Yin brush ba shine abu mafi muhimmanci ba, yin brush ba shine abu mafi muhimmanci ba, a'a, yin brush din bisa ka'idar yadda ake yinsa shine mafi muhimmanci. 
Da yawan mu mun dauka cewa kawai idan idan munzo yin brush, da zarar munga bakin mu yayi kumfa yayin wanke hakora shikenan mun wanke bakin mu, alhalin ba haka bane. Mu kasance masu ziyartar asibitin hakora domin samun shawarwarin likita akan yadda zamu rinka kula da hakoran mu. 

A karshe, mu tuna da cewa "oral health is the key to the general health" 
Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post